(ABNA24.com) Babban kwamandan dakarun juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran Manjo Janar Husain Salami ya yabawa hukumar gidajen radiyo da talabijin ta kasar Iran kan gagarumin kokarin da take yi don isar da gaskiya a ko ina a duniya, ya kuma kwatanta hukumar da rana, wacce, duk tare da kankantarta tana haskanan ko ina a duniya.
Janar Salami wanda ya gabatarwa da jawabi a wani taron girmamawasu yan jaridu na hukumar gidajen radiyo da talabijin ta kasar a dakin taro na hukumar da ke nan Tehran a yau Lahadi, ya kara da cewa gwamnatin kasar Amurka tana son mutanen duniya su ci gaba da kasancewa cikin duhu, dangane da lamuran da suka tafiya a duniya, amma duk tare da karancin kayan aiki da kuma kudade wanda hukumar IRIB ta ke fama das u, ta sami nasarori masu yawa wajen isar da gaskiya ga mutaneda dama a duniya.
Shima shugaban hukmar Abdol Ali Ali-Askari, a cikin jawabinsa a taron ya yi kira ga yan jaridu na hukumar da su yi kokarin gano irin hanyoyin da makiya suke bi wajen yakar kwakwalen mutane a duniya don fuskantarsu ta hanyoyin da suka dace.
/129
7 Oktoba 2019 - 05:20
Lambar labari: 980758
Babban kwamandan dakarun juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran Manjo Janar Husain Salami ya yabawa hukumar gidajen radiyo da talabijin ta kasar Iran kan gagarumin kokarin da take yi don isar da gaskiya a ko ina a duniya,...